Main menu

Pages

YADDA AKE HADIN SABAYA DON MURJEWAN JIKI DA TAYAR DA BRST DIN DA YA ZUBE







CIKAKKEN BAYANIN YADDA AKE HADIN SABAYA

Abubuwan da za a nema don hada sabaya

- Alkama

- Waken Soya

- Danyar Shinkafa

- Gyada (kamfala)

- Ridi

- Hulba

- Madara

- Zuma/Sugar


Measurements

Alkama, danyar shinkafa, Waken suya dukkansu kwano dai dai. 


Ridi, Gyada da Hulba Rabin kwano kowane.


Yadda ake hadawa;

Za a jiqa alkama da danyar shinkafa waje daya na tsawon awa biyar. 


Shi Kuma Gyada da Ridi a hadesu waje daya a soya, sama sama a bushe bawon gyadar.


Sai a tsame shinkafa da alkaman nan idan sunntsane sai a hadesu da wannan soyayyen Ridi da Gyada da waken soya da Hulba akai inji a niko miki.


Idan an kawo garin sai ki ringa dama cokaki ukku kullum safe da yamma kina sha. Wajen damawar zaki dama ne kamar zaki talge.


Idan kin sauke sai kisa Madara da Zuma ko sugar ki ringa sha.



Wannan hadi yana tayar da brst sosai ko shayarwa kike ba abinda nononki zai yi zai tsaya kyam Insha Allah.


Sannan yana gyara jiki kiyi sumul sumul kamar jiki kulba kiyi fresh sannan zaki murje duk wata rama Insha Allah.

Comments