Main menu

Pages

ABIN MAMAKI; TA ZABI TA AURI KARENTA DA TA AURI MUTUM




 Abin Mamaki; Matar Da ta Auri Karenta Shekara 11 Da suka wuce, Tace Ya Fiye mata Kasancewa Da Mutum.


Matar da ta auri Karenta tace don dai Mutane suna yu mata kallon mara hankali, Amma ita fa rayuwa da Karenta yafi mata komai.



Wilhelmina Morgan Callaghan wadda take cikin shekaru 40 ta fito ne daga Arewacin Ireland. Ta auri Karenta Henry shekara 11 da suka wuce.


Duk mun san cewa kare shine kusan babban abokin mutane (kar ma can kasar turawa da suke ba kare muhimmanci fiye da komai.) Callaghan ta yaba halayen Henry ta yadda yake dauke mata kewa da damuwa a lokacin da take cikin qunci.



Abubuwa sun lalace ne tun lokacin  da sukai aure 2009, tace "Ta rasa aikinta a morgue, don haka dole ta zama Mai aikin wucin gadi na shirya gawawwaki a matuary, Kuma ba wasu kudi take samu sosai ba a wannan aikin, sannan ga gidan ta duk kusan ruwa ya lalata shi wani wurin ya fada.


Amma Henry ya taka muhimmiyar rawa a cikin wannan hali, yana bata gudummuwa sosai sannan ta Kara da Kiran shi "RI" ma'ana "King" saboda shi din kamar Sarki ne a wajenta.

Comments