Yadda Zaki Qamsasa jikinki cikin sauqi.
Da farko a zuba lalle a tukunya a sa ruwa, a dora a wuta ya dahu sosai, sai a sauke, a tace, sannan a cire garin lalle gefe sai a mayar da ruwan kan wuta, a rage wuta sai a kawo madarar turare na sandal bakhur, damarar Ledus da madara Musk,
Sannan a bari ya tafasa sosai, sannan a sauke, in ya huce ki nemi jarka ko galan mai cin lita hudu ki juye a ciki, duk sanda ki ka yi wanka, in kin gama sai ki kawo wannan hadin ki zuba kadan a bokiti, sai ki kara ruwa kadan sai ki dauraye jikinki da shi, kar ki goge jiki ki bar shi ya bushe.
Za ki sha mamakin yadda kamshin zai zauna a jikinki. Sannan kuma ku zamto masu yawan mu’amalla da turare a koda yaushe, in har kun san baku da hanyar wadannan to ku zama masu yawan sa turaruka a wurare shida kullum a jikin ku.
Bayan kunnenku
Dantse
Sharaba
Wuya
kasan nono da sauransu.
Gaban ku kuma ku dan samu auduga ku jikata da madarar misk (Aisha) sai a dinga matsi dashi, haka zaisa shima gabanki (farji) ya dinga diban kamshi.
Comments
Post a Comment