ME YAKE KAWO JINKIRIN JININ HAILA KO JININ AL'ADA GA MATA (AMENORRHEA)
JINKIRIN HAILA : shi ne samun tsaiko ko jinkirin al’ada tsawon wata biyu ko fiye da haka.
Jinkirin Haila Ya kasu kashi uku 3 :
1- Primary Amenorrhea
2- Secondary Amenorrhea
3- Spiritually Amenorrhea
1- primary Amenorrhea : shine jinkirin rashin yin hailar mace har takai shekaru goma sha shidda zuwa sama bata fara haila ba.
2- Secondary Amenorrhea : shine macen da dama Chan tana ganin hailarta normal sai yadaina zuwa mata.
3- Spritually Amenorrhea
Shine daukewar jinin Haila a dalilin shafar shedanun Aljanu ko sihiri ko cututtukan Aljanu
MEYAKE KAWO JINKRIN HAILA??
abubuwa da dama suna kawo jinkirin Haila, ga kadan daga ciki :
1- Pregnancy.
Mafi yawan mata idan sun dauki ciki sun daina ganin hailarsu.
2- Lactating
Akoi mata da dama idan suna shayarwa basa ganin hailarsu.
3- Infection
Yana daga cikin abubuwanda yake kawo jinkirin Haila sun hada da shigar kwayoyin cuta a mahaifa, kamar ta hanyar kamuwa da ciwon sanyi.
4- Family Planning Pills
Shan wassu daga cikin kwayoyin hutun haihuwa (a cikinsu akwai masu rikita haila, akwai kuma wadanda suke saita Haila )
5- Family planning injection e.g Depo-provera.
Amfanin da allurar hutun haihuwa kamar su Depo Provera.
6- ovarian cyst
kumburin kwan mace da ake cewa ovarian cyst shima yana rikitar da Haila.
7- Stress
Rashin kwanciyar hankali kaga mace kullum ta tada hanakalinta akan wani Abu shima yana rikitar da Haila.
8- Regular Strenuous Exercise.
Motsa jiki mai tada hanakali kamar gudu zuwa waje mai Nisa.
9- Extremely Low Body Weight.
Rashin nauyin jiki wanda ake samu Sabida rashin isheshahen abinci lafiyayye.
10- Diseases
Wasu cututtuka kamar su zazzabin typhoid, ko tari.
11- Problem with thyroid
Masalar thyroid gland wanda yake kawo hormones.
12- Then certain types of medicine, such as antidepressants, chemotherapy etc.
13- Tasirin Shedanun aljanu a jiki
Wadannan abubuwan duk suna kawo matsalar Al'ada jinkirinta ko rikicewarta don haka sai mu kula.
Comments
Post a Comment