ABBW GUDA 4 DA SUKE SAURIN LALATA AURE
1.KISHI MAI TSANANI. Idan kishi ya yi tsanani da yawa sai ya zama matsala ga mai shi da kuma wanda ake kishin a kansa.
2. SA IDO DA BIBIYA. Sa ido muguwar sana'a, duk wanda ya sa maka ido, yake bibiyarka, ya ke neman aibinka ko kuskuran ka ko kasawar ka, ko laifinka, wannan ba masoyin ka bane na gaskiya.
3. NUNA FIFIKO DA ISA AKAN JUNA. Nuna fifiko da isa, yana jawo raini, da wulakanci, da rashin ƙimantawa babu kuwa mai son a wulakanta shi, duk sanda ma'aurata, miji ko mata ya raina abokin zamansa, to zama ba zai yiyuba a wannan hali, dole a sami cikas,
4. YAWAN ZARGI. Yawan zargi ba tare da dalili ba, yana rushe kauna, da aminci tsakanin ma'aurata, daganan sai dangantaka ta yi tsami har ya kai ga rushewar aure.
Comments
Post a Comment