A YI MA RUKAYYA DA YARANTA ADALCI TA HANYAR NEMO WADANDA SUKA KASHE TA
Innalillahi Wa'inna Ilayhirrajiun Rajiun
Anyimata KISAN GILLA ba tareda Hakkinta ba.
An samu Rukayya Kano a ranar Asabar 12 - 02 - 2022 cikin Jini shame-shame a kwance ita da Yaranta yayinda aka shiga gidanta da yammacin Ranar Asabar.
Tun fitar Maigidanta da Safe aka shiga Gidanta dake Unguwar Danbare gaban Rijiyar Zaki a Jihar Kano da Kayan Barchi ajikinta aka yimata Kisan Gilla ta hanyar Tanfatsa Mata tabarya da aka dingayi akanta wanda har saida aka fasa mata goshinta sa'annan kuma aka yanketa da wuka wurare daban daban ajikinta sannan Yaranta guda 2 da Dan shekara 3 aka yimasa Yanka Mummuna da kuma Yar Shekara 1 da ake goya ta itama aka yimata yanka Mummuna.
Yaran basu Mutu ba amman Mamansu ta Mutu tun a lokacin har yammaci da aka shiga gidan aka ganta kwance cikin Jini Shame-shame duk ya bushe Rukayya ta sandare tuni yaranta sunyi kuka sun gaji sunyi Barchi anan sun tashi sun koma yayinda aka samesu. Yanzu yaran suna Asibiti ita kuma Rukayya Kano tun a safiyar Yau Ranar Lahadi 13 - 02 - 2022 akayimata Jana'iza aka binneta.
Rabon da naga Kisan Gilla Mummuna tun Kisan da akayiwa Hajiya Sa'adatu Rimi a Kano Allah yayimusu Rahama.
Muna rokon Shugabanni da Jami'ai akan a cigaba da bin kadi wajen ganin an nemo wadannan Azzalumai, Allah ka tsine musu ka wulakanta su tun anan Duniya da kuma Lahira.
A'lummah mu cigaba da yadawa mu sauke nauyinmu harsai munga cewar mun sanya an nemowa Rukayya Kano da Yay'anta hakkinsu da aka kashe ta bada hakkinta ba.
Allah kayiwa Rukayya Kano Sakayya da Yaranta kayimata Rahama Ya Allah
Comments
Post a Comment