YANZU-YANZU: ASUU Ta Ayyana Sheikh Isah Ali Pantami A Matsayin Farfesan Bogi.
Ƙungiyar bayan taronta na Majalisar Zartaswa ta ƙasa ta ayyana ƙarin girman a matsayi na Farfesa an yi ne "ba bisa ƙa'ida ba".
An bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya yi jawabi a ranar Litinin kamar yarda Daily True Hausa ta ruwaito.
Ya ce, “Ba za ka iya zama minista kuma ka zama malami a jami’a ba".
“Dole ne Pantami ya ajiye aiki a matsayin minista kuma a sake gwada shi saboda Bai cancanta ba, Bai kamata a dauki Pantami a matsayin farfesa ba."
A watan Satumbar 2021, Majalisar Jami'ar Fasaha ta Tarayya, Owerri ta daukaka Pantami, tare da malamai bakwai zuwa matsayin farfesa a taron majalisar karo na 186.
Comments
Post a Comment