Main menu

Pages

CIKIN AMFANIN DA GANYEN MAGARYA KEYI KO KUNSAN WANNAN?

 



AMFANIN GARIN MAGARYA GA LAFIYAR MU

- Ciwon daji (cancer) : Idan ana dafa garin magarya anasha da zuma yana kashe kwayar cutar daji koda na cikin jini ne idan kuma Yayi gyanbo sai arinka dafa garin magaryar da ruwan khal ana wanke wurin gyanbon idan an wanke sai a barbada garin magaryar.


- Yanada karfin yaqar cutar fata kamar su tautau, makero, qazuwa da sauransu sai akwaba shi da zuma a rika sha Ana shafawa a wurin da ciwon yake.


- Yana tsaftace jini domin yana dauke da sinadarin Saponin, alkaloid da triterpenoid wadannan sinadaraine masu tsaftace Jini.


- Shansa da ruwan zafi yana magance gajiya da ciwon jiki.


- Yana magance ulcer idan ana shansa da madara ko zuma.


- Yana taimakawa hanta ya hanata jin ciwo da kamuwa da cututtuka.


- Yana daidaita nauyin mutun.


- Yana tsaida zawo cikin kankanin lokaci idan aka Sha shi da ruwa ko koko.


- Yana miqar da kasusuwa musamman ga mai karaya.


- Yana maganin rashin shaawa ga mata idan suna tsarki da ruwan duminsa kuma Suna shansa da Madara.

Comments