ABUBUWA GOMA MASU LALATA ZUCIYA
Duk wanda ya dabi'antu da daya daga cikin wadannan suffofi to kuwa, ya dau hanyar gurbata zuciyarsa.
1- Yawan magana marar amfani tare da rashin ambaton Allah mai yawa.
2- Rashin kulawa da maraya da mai karamin karfi.
3- Yawan dariya da rashin yin kuka dan tuna girma Allah.
4- Yawan cin abinci musammama idan daga dukiyar haramunne.
5- Yawan Sabon Allah kuma babu yawaita tuba da istighfari.
6- San zuciya da bin Sha'awar zuciya.
7- Rashin kyautata Sallah
8- Sanun duniya da rashin tuna mutuwa.
9-Rashin karanta alqurani da rashin kokarin sanin ma'anoninsa.
10-Rashin Neman ilimi da aiki da shi.
Allah Shi ne mafi sani
Ya Allah mai jujjuya zukata,ka tabbatar da zukatan mu akan addininKa.
Comments
Post a Comment