Main menu

Pages

INA UWARGIDA DA AMARYA, KU KOYI YADDA AKE DAFA 'YAN SHILA




Dahuwar 'Yan Shila Don Qarin Ni'ima

-- ‘Yan shila guda biyu.

-- Albasa fara.

-- Gyadar mata.

-- Furen zogale.

-- Idon zakara.

-- Kayan qanshi.

Zaki hade wadannan abubuwan duka ki dake su waje daya, (gyadar Mata, Furen zogale, Idon zakara, da kayan qamshi).


Sannan ki gyara 'yan Shilanki, bayan kin wanke sai ki dora tukunya kisa ruwa dai dai gwargwado, sannan ki zuba duka duka wadannan kayan hadi ki Saka 'yan shilan kisa sinadarin dandano da Dan gishir kadan ki yayyanka wannan Farar albasan ki barshi yayi ta dahuwar. 


Ki tabbatar kin dafa wannan ‘yan shila da wadannan kayayyakin ba daga baya kka zuba ba, so ake su dahu tare don su shiga cikin naman sosai. Sannan abinda akeso shine ya zamto dasu kika fara karyawa da safe, yana matuqar qara kwarjini da ni’ima.

Comments