YANDA AKE YIN MADARAR WAKEN SOYA.
Mataki Na - 1
Za a fitar da duk wani datti da aka san yana jikin Waken Soya din, a kuma tabbatar babu dattin a ciki duk an kautar da shi.
.
Mataki Na - 2
Za a sanya ruwa a kan Wuta ya tafasa, idan y kammala tafasa sai a dauko Waken Soyan nan da aka gama tsincewa a zuba a cikin wannan ruwan zafin, sai a dunga juyawa da Cokalin miya har sai ya dibi kimanin mintuna 10 haka. Sannn sai a sauke.
.
Mataki Na - 3
Idan an sauke, za a zuba a cikin Kwandon tace Shinkafa. Kunga kenan ruwan zafin da yake ciki zai tsiyaye a kasa, to sai a dauko ruwan sanyi a yayyafa akan Waken Soyan, Amma ruwan sanyin kadan-kadan fa. Domin hakan zai taimaka Bawon jikin Waken Soyan ya tattaso sama tunda ya jiku.
.
Mataki Na - 4.
Sai a saka hannu duk biyun a dunga murje Waken na yanda duk za a fitar da bawon jikin Waken Soyan. Kamar dai yanda ake yiwa Waken yin Alala, ko kuma Kosai. Idan an kammala fitar da Bawan sai a wanke Waken Soyan sosai da sosai.
.
Mataki Na - 5
Za a dora ruwa a kan Wuta a karo na biyu kenan, sannan sai a bar ruwan ya tafasa, idan anga ya tafasa, sai a dauko wannan Waken Soyan da aka kammala wankewa sai a zuba a cikin tafashash-shen ruwan, sannan sai a dunga juyawa har zuwa lokacin da za a ga Waken ya dahu. Yana iya daukan mintuna 25 ko fiye da haka kafin ya dahon. ( A lura. Ruwan da za a dunga zuba Waken a ciki dole ya dunga zama wadatacce ne yanda bazai yiwa Waken kadan ba )
.
Mataki Na - 6.
Idan an kammala dafa Waken Soyan, sai a sauke, sannan a tace ruwan, za a ga Waken Soyan duk ya babbare bibbiyu, kamar dai gyada a barata biyu hakan zai zama. To sai a barshi duk ruwan ya gama tsanewa gaba daya.
.
Mataki Na - 7
A wannan Matakin dole a lura sosai domin shine matakin da ake bi wajen busar da wannan Waken Soyan da aka kammala dafawa yanzu.
*- Za a iyi busarwa da zafin rana
*- Za a iya busarwa da zafin Oven
*- Za a iya busarwa da prawn
*- Za a iya busarwa da duk wata hanya da aka san idan an busar dashi zai bushe sosai da sosai.
.
Mataki Na - 8
Idan ya gama bushewa, sai a dauko shi a zuba a cikin Blendar a hada da sugar da Madarar gari adadin quater idan na kwano daya ne, a nika sosai da sosai. A tabbatar nikan yayi laushi sosai fa. Idan an gama nikawa sai a dauko abin tankadewa mai laushi sai a tankade yanda zayyi laushi da gaske.
.
Za a sami mazubi mai murfi sai a zuba a ciki a kuma rufe. Za a iya daukan watanni uku a na amfani da Ita kadan-kadan.
.
Comments
Post a Comment