Main menu

Pages

KO KINSAN YADDA AKE HADA TURAREN WUTA NA DAKI?




TURAREN WUTA NA DAKI

Yadda ake hada irin Wannan turaren wuta shine Zaki tanadi wadannan abubuwan

◦ Farce

◦ Sukari

◦ Lemon tsami

◦ Jawul fari

◦ Misik

◦ Garin sandol

◦ Madarar turaren jamila

◦ Madarar turaren wanis

◦ Madarar turaren sabon yayi

◦ Madarar turaren binta sudan

◦ Madarar turaren kamfani

◦ Madarar turaren naludu

◦ Madarar turaren dan duwala

◦ Madarar turaren kafin kafi

◦ Madarar turaren sandol

◦ Madarar turaren abarai dadi

◦ Turaren ruwa mai maiko

yadda zaki yi ki sami itacen al'ud dinki daya, ko biyu sai ki jika shi da madarar turaren jamila da madarar turaren wanis, da madarar turaren sabon yayi, sannan ki sa turarenki mai maiko na ruwa irin wanda ake aunawa a dogwayen kwalabe sai ki jika da wadannan turaruka ki rufe ki bar shi ya jiku har yayi kwana, bakwai. 


 Bayan sati daya sai ki bude itacen alud din da kika jika da turare, idan kuma kilo daya ne sai ki sa gwangwani daya, idan sukarin gwangwani biyu ne sai ki zuba ruwa cikin karamin kofi ki matsa lemon tsami hudu a kan ruwan sukari, idan kuma gwangwani daya ne sai ki zuba ruwa rabin karamin kofi ki matsa lemon tsami biyu a kai sannan ki saka garin jawul cokali daya da ruwan lemon tsami da sukarin ki sa misik kwaya uku a ciki, sannan ki debi garin farcen da kika barza ki zuba kadan a kai amma shi ma farcen zaki gyara shi.


kamar irin gyaran da aka ce za'a yi masa a hadin humra, sai dai shi bayan an soye an barje shi ba daka shi lukwi ake yi ba idan kin zuba sai ki bar shi yayi ta dahuwa har sai ruwan sukarin ya fara ja,sannan ki zuba itacen al'aud din naki a kai kiyi ta juyawa idan ya dahu sosai sai ki sauke ki juye a faranti ki baza

sannan ki zuba garin sandol dinki a kai da garin dakakken misik da garin dakakken jawul.

Comments

1 comment
Post a Comment
  1. Slots | Casino in Lisbon, Lisbon, Portugal
    › news › news 슬롯머신 게임 Slots is 암호화폐란 the fastest growing casino and 사이트추천 slot machine game in the world. Players 검증 업체 먹튀 랭크 can enjoy more than 1000 slots games such as 바카라 용어 video slots and casino games.

    ReplyDelete

Post a Comment