AMFANIN GORIBA GA LAFIYAR MU
- Tana maganin jiri. mai fama da jiri ko jiwa zai koneta ya rinka shekar hayakin kwallon na yan mintuna.
- Masu ciwon asthma zasu koneta bayan ta kone se a dake a dibi rabin cokali a zuba a tafashasshen ruwa kofi daya bayan minti goma, se asha. Za'a yi haka sau uku.
- Cinta hakanan na kara ma hakori karfi da qashi domin akwai sinadarin culsium a cikin ta.
- Cinta hakanan ya na karama maza kuzari da karfin jima'i ga namiji kuma tana kara yawan ruwan maniyi, musamman idan za a yi lemunta.
- Cinta hakanan tana maganin basir mai tsuro da wanda ba mai tsuro ba.
- Masu sanko ko wanda gashinsu ke zubewa su jikata idan ta jiku su rinka wanke kai da shi.
- Cinta rigakafi ne ga cutar daji wato cancer.
- Tana magance hawan jini idan aka dake garinta ya yi lukwi2 aka tankade se a zuba babban cokali daya a ruwa ya jiku se a tace a sha, za'a maimata har sau uku a rana.
- Cinta hakanan na rage kitse a jiki ma'ana yana rage timbi da qiba.
- Cinta hakanan na matsayin rigakafin kamuwa da ciwon zuciya.
Allah yasa mu dace
Comments
Post a Comment