LOKACIN KARBAR ADDU'A A RANAR JUMA'A
Manzon Allah SAW yace:"A (Ranar) Juma'a a kwai wani lokaci da babu wani bawa musulmi da zai dace da ita, yana a tsaye yana sallah, sai ya rok'i Allah wani alkhairi face Allah ya bashi". Bukhary da Muslim
Abin da a ke nufi da "Yana tsaye yana sallah" ai yana zaune yana jiran sallah, yana ambaton Allah kuma yana addu'a, domin wanda ya zauna a masallaci yana jiran sallah to yana cikin sallah ne".
Shaykh Bn Bazz RA yace:
"Wannan lokacin shine bayan sallar la'asar har zuwa faduwar rana ga wanda ya zauna yana jiran sallar magriba, a masallaci ne ko a gida, mace ne ko namiji ya zauna yana jiran lokacin amsar addu'a, sai dai namiji ba zai yi sallar magriba a gida ba ko ma sauran salloli(na farillah) face da wani uzuri da Shari'a ta yarda dashi..."
مجموع فتاوى ومقالات الشيخ ابن باز (6/159)
Comments
Post a Comment