Main menu

Pages

MAGANIN CUTAR SUGAR DA HAWAN JINI



Fa'idar Ganyen Mangwaro Wajen Maganin cutar Sugar (Diabetes) Da Kuma Saukar Da Hawan Jini.

Masana ilimin kimiyyar magunguna, na kasar Sin da India, sun tabbatar da cewar daya daga cikin manyan magungunan warkar da ciwon suga (diabetes) shine Ganyen Mangwaro?


Ganyen Mangwaro na dauke da sinadarai masu yawan gaske da ke amfana wa jikin Dan’adam, amma kash, mutane da dama basu san hakan ba!


Yadda ake amfani da shi a matsayin Maganin cutar ciwon Suga ( Diabetes)

(1) A tsinko ganyan Mangwaro,masu kyau. A wanke su sosai

(2) A sanya ruwa a murhu, a tafasashi, har na tsawon minti biyar ba tare da ganyen ba.

(3) Sai a zuba ganyen a cikin ruwan zafin da ke kan murhu,tare da OLIVE Oil (wato Man Zaitun). A barshi yayi ta tafasa, har na tsawon mintuna biyar zuwa goma.

(4) Sai a sauke shi a tace.

(5) Sai a sanya shi cikin kwano ko gilashi mai kyau, a barshi ya kwana

(6) Sai a sha wannan ruwan da sassafe bayan an tashi daga barci, kafin ka ci komai.

.

Wannan maganin, yana kawar da abubuwa (marasa kyau masu guba) daga jikin mutum, kuma yana rage yawan suga da ke cikin jini. Haka kuma yana saukar da hawan jini.


Allah Yasa a dace

Comments