Sabon Tsarin MTN Data Na N200/1G na Wannan Shekaran.
MTN Data na Naira 200 ga 1G na Wannan Shekaran 2022 yana daga cikin mafi sauqin tsarin data da za a iya samun shi a Nigeria. Tsarin ne na garabasa daga company MTN Nigeria don samar da sassauqar data ga mutanen da basa iya sanya babban tsarin Data ko kuma suka fi son data mafi sauqi da sayen manyan.
Kamar dai yadda kowa ya sani shine hanyar sayen data a company MTN shine ta hanyar danna lambobi kamar haka *131#, ta wannan hanyar za ka iya samun wasu tsare -tsaren sayen data da farashinsu, (Amma ba duka tsarin za a iya samu ba).
Za a iya bi ta wannan hanyar (*131#) don shiga cikin tsarin 200/1G. Amma idan aka yi amfani da lambobin ta mobile dialer wato ta wajen kira a waya, to fa bazai ka gano tsarin ba. Don haka zan nuna maku yadda zakuyi amfani da code din don shiga tsarin, tare da wasu tsare - tsaren masu sauqi
Kafin nan ya kamata na fada maku abubuwa da ya kamata ace Sim din na dashi don shiga wannan tsari na samun data cikin sauqi.
Abubuwa da ake buqatar sim dinku dasu kafin shiga tsarin sune;
- Dole ne ya zamto Sim card din yana aiki Kuma Kuma Yana da register sannan ya zaman to an hada shi da NIN.
- Ya zaman to kana kan tsarin MTN Pulse tariff Plan.
- A qalla ya zamto akwai N200 a cikin account balance dinka
Idan kana da wadannan abubuwan na sama to Insha Allah za ka iya shiga wannan tsari.
Idan baka cikin tsarin MTN Pulse, to ga yadda za kayi migrating;
- Ka Sanya code na pulse migrating *406# kayi sending da MTN line dinka
Daga nan zakayi replying da "I" sai ka zabi migrate to pulse. ( Za a turo maka saqo immediately na cewa ka shiga tsarin pulse) Kuma wannan migrating din free ne ba wani charges.
To yanzu Kuma ga yadda za Kai activating data N200 for 1G
Ka shiga wajen kira a wayarka ka danna *131*65# ka tura da layin ka na MTN.
Za kayi reply da 1,2 ko 3 na tsarin da zakayi, idan tsarin number 1 ne sai Kai reply da 1, idan number 2 ne haka ma in number 3 ne ya danganta da tsarin da ka saya.
Idan kayi amfani da *131*65# bai yiba, to kar ka damu. Ka Sanya *131*25#
Duk Wanda ya biyo wannan tsarin tun farko har qarshe bai yi ba (Wanda hkan ma da wuya) but in case to yamin magana zan qara yo typing akan hanya ta biyu wadda zaka samu cheapest Data Insha Allah.
Comments
Post a Comment