Main menu

Pages

SIRRIN AMFANI DA SHAMAR(FUNNEL SEEDS)



SIRRIN AMFANIDA SHAMAR

A cikin 'ya'yan itace wanda sukeda dogon tarihi a magungunan Muslunci da akwai wani me suna SHAMAR wato (fennal seed) a yaren nasara yana kama da alkama amma sufar jikinsa kuma kamar kubewa yake yafi samuwa  a kudancin nahiyar afirka, koda yake ayanzu ya zagaya ko ina,



Idan kina gudun samun matsalar nono ko ciwon nono ta dalilin shayarwa to kina tafasa shayinsa da 'ya'yan hulba kina sha safe da yamma koda kina shayarwa ki jarraba, domin yana yakar cututtukan dake haddasa kansa, sannan bazai bari su lalaceba,



Idan kuma gashi akeso a gyara dashi to ayi amfani dashi da garin zaitun a kwaba ana shafawa lokacinda aka wanke kai, su kuma wadan da keson rage teba suyi amfani da shayinsa da na'a na'a kullum da safe kafin aci abinci,




Idan ana maganar akan abunda akafi aiki dashi shine shayi domin wasu da yawa suna shayinsa ne ma amatsayin kayan kamshi amma kuma sashin maganine dake kara karfin ido tare da narkar da kitse a jikin mutum har ma ana fadar yanda ya ke rike ciki mutum ba zaiyi yawan cin abinci ba,





Idan kuma akayi garinsa ana hadawa da garin bagaruwar hausa anasha da shayi ko kuma da nono a matsayin maganin olsa sadidan wanda ke aiki da zaran an farasha.

Comments