Main menu

Pages

TABDI!! KO KUNSAN CIN GASASSHEN NAMA ZALLA NA HAIFAR DA MATSALA

 



Cin Gashasshen Nama Zalla Na Haifar Da Matsala

Masana; Wata Farfesa akan ilimin lafiyar jama’a da abinci da ke jami’ar Nijeriya Nsukka ta gargadi mutane da su guji cin nama gasasshe (Balangu ko tsire) zallan shi ba tare da an hada shi da kayan miya ko ganyayyaki kamar kabeji da Albasa ba.


Masaniyar mai suna farfesa Ngozi Nnam ta ce cin gasasshen nama haka kawai ba tare da irin wadannan hadin ba na iya haifar da cutar daji.


Ta bayyana cewa wannan ya na faruwa ne saboda hayakin da naman ya ke nada yayin da ake gasa shi, wanda ke dauke da wani dafi da ka iya haifar da cutar.


Ta ce amma idan aka hada naman da kabeji, ko wasu ganyayyakin daban, toh suna taimakawa wajen kashe karfin dafin.


Baya ga wannan, farfesar ta kuma yi kira da a kula da kifi shi ma domin gasa shi na sa ya samu irin wannna dafin da ke haifar da cutar ta daji.

Comments