Main menu

Pages

TARIN FALALA DA ALKHAIRAN DAKE CIKIN WANNAN LKCN NA HUNTURU

 


MU RIBACI WANNAN LOKACI NA HUNTURU DA IBADAH


Lokacin Hunturu Lokacin ne da Ubangiji Yake Tsawaita Dare Don Masu Bauta Na Haƙiƙa Su Dage dayi Masa Bauta a Cikinsa. Bautar da ta Ƙunshi Tun Daga Tsayuwar Dare Har Zuwa Karatun Alƙur'ani, Bayan Mutum Ya Samu Isashshen Bacci Saboda Yanda Daren Yake da Tsawo.


Sannan Aka Taƙaita Yini Don Muminai Su Azumceshi. Gashi Yinin An Taƙaitashi Sannan Kuma Babu Zafin Ranan da Zata Jigata Mai Azumi Kamar Sauran Lokutan da ba Hunturu ba. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:


 عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: (الصيام في الشتاء الغنيمة الباردة)

[رواه الترمذي]


Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa; “Azumi Lokacin Hunturu Ganima Ce Cikin Ruwan Sanyi (Ba Tare da Yaƙi ba".

(Tirmizi Ya Ruwaitoshi)


Lallai Idan Mukayi Duba da Wannan Hadisin Zamu Fahimci Yin Sakaci Wannan Ganimar ta Kuɓuce Mana, Ba Ƙaramar Asara Zamu Tafka ba. Hasanul Basary (rh) Yana Cewa:


قال الإمام حسن البصري (نعم زمان المؤمن الشتاء، ليله طويل يقومه، ونهاره قصير يصومه)


Hasanul Basary Yana Cewa: “Madallah da Lokacin Zunturu ga Mumini. Darensa Yanada tsawon da Yake Rayashi. Yininsa Kuma Taƙaitacce ne Yana Azumtarsa".


Ibn Mas'ud (ra) Yana Cewa:


قال ابن مسعود رضي الله عنه : (مرحبا بالشتاء تنزل فيه البركة ويطول فيه الليل للقيام، ويقصر فيه النهار للصيام)


“Maraba da Lokacin Hunturu, Albarka Yana Sauka a Cikinsa. Kuma Darensa Yana Tsawaita Don a Rayashi. Yininsa Kuma Ya Taƙaita Don a Azumceshi".


Har Ubaid bn Umair (rh) Yana Cewa:


"يا أهل القرآن: طال ليلكم لقراءتكم فاقرءوا، وقصر النهار لصيامكم فصوموا“


“Yaku Ma'abota Alƙur'ani Dare Ya Tsawaita Gareku Don Karatunku, To Kuyi Karatu a Cikinsa. Kuma Yini Ya Taƙaita Don Azuminku To Ku Azumceshi".


Umar bn Khaɗɗab (ra) Yana Cewa:


قال عمر رضي الله عنه: (الشتاء غنيمة العابدين)


“Lokacin Hunturu Ganima Ce Ga Masu Bauta".


Yar Uwa/Ɗan Uwa Idan kuna Buƙatar Kasancewa Cikin Bayin Allah Nagari, Kiyi/Kayi Ƙoƙari Ka Yaƙi Zuciyarka domin Ribaci Wannan Lokaci Mai Albarka. Sau Ɗaya Yake zuwa a Shekara; Tayiwu Wannan Hunturun Shine Na Ƙarshe a Rayuwarki/ka To Kayi Amfani da Wannan Damar ta Rai da Lafiya da Ubangiji ya Baka Ka Amfana da Wannan Ganimar.


ALLAH UBANGIJI KA BAMU LAFIYA DA IKON RIBATAR WANNAN LOKACI MAI ALBARKA. AMEEN.

Comments