Main menu

Pages

WANN SHINE GARIN DA FATALWA KE CIN KAREN SU BA BABBAKA.

 

Ku Kalli Wannan Garin Shine Garin Da kowane Gini Yake da Fatalwar da Ke Zaune Tana rayuwa a Ciki.


Richmond na daya daga cikin tsoffin garuruwan dake America, kuma duk yawancin gine - ginen dake cikin garin suna nan tun tsawon lokacin da aka gina su.



A birnin Richmond, za ka gane cewa akwai tsaface - tsafacen da akai da kuma masu bugun qasa da anan ake cema 'yan duba, duk sun tattara a kasar Fort Bend, birnin da ya qara bunqasa a shekaran 1837. Kamar yadda al'umma da yawa suka gudana dogon tarihi da na masu arziki, to ba abin mamaki bane in wannan gari ya zamto mafakar masu farautar fatalwa da masu believing akan Sauran abubuwa na tsaface - tsaface.


Indai kana neman duk Wani abu da ya shafi fatalwa da aljanu to Richmond shine garin da zakaje, inji Mayor Becky Hass. Hass yasan abubuwa da yawa da suka hada da yada tarihin kasuwanci da labarin fatalwowin dake Richmond.



A unguwar Morton kunshe take da hada hada. To kowane gini dake unguwar yana da fatalwa a Ciki saboda dadewar da sukai. Inji Mayor.


Akwai wata hanya wadda fatalwowin ke biyowa ta nan suke zirga zirgansu, to cikin dare ana ganin wani haske tsanwa yana bayyana kullum dare.


Daga bayan wurin Kuma akwai abubuwa da suke reflecting Wanda ba Wanda zai iya gane dalilin kasancewar hasken a wajen.


Amma wasu sunce wai matattun wajen ne saboda tsohuwar macuware ne a wsjen.


Akwai Wani gidan cin abinci Sandy McGee dake Jin abubawa da ya shafi fatalwowin.


Kusa da gidan abincin Sandy McGee akwai Wani gidan shakatawa, wanda ya dauki kusan shekara 120 da ginawa, farkon ginin kamfanin motoci ne, sannan aka maida shi post office, sannan a karshe ya zama wajen cin abinci a yanzu.


Daga ciki suna Jin kamar Wani abu na binsu, sannan kujerun wajen na motsawa da kansu.


Akwai lokacin da aka ringa Jin hayaniya da surutai alhalin ba kowa a cikin ginin, sannan zakaji dariyar mace da ire iren abubuwan ban tsoro. Amma ba a taba cutar da kowa ba, don haka ake zaton wadannan fatalwowi ba masu cutarwa bane inji mamallakin Sandy McGee.


Sannan akwai wata nurse da ta taba hango Fatalwar a sigar mutum a can Saman bene ya shiga wani daki.

Comments