YADDA AKE HADA TURARE NA KAYA DA NA TSUGUNO {culucture} HADIN HUMAR
FARAR HUMRA
turaren alajin na ruwa ko na marakana ko na matan arewa
✭ jan ambur
✭ farin ambur
✭ misik
✭ madarar turaren kwamando
✭ madarar turaren suzan
✭ madarar turaren sarkin turare
✭ madarar turaren sandol
✭ madarar turaren ismiyaki
zaki daka farin ambar dinki wanda ake sayarwa a kasuwa guda uku,
sannan ki daka jan dan kanti guda uku, sai ki zuba a kan ruwan turaren alajin, ko marajana ko matan arewa roba daya, ki sami miski dinki guda hudu ki zuba a kofin silver ko a tukunyar silver ki dora a kan garwashi zai narke.
idan ya narke sai ki yi sauri ki juye a cikin ruwan turaren da kika zuba garin abubuwan, sannan ki daka misik din ki sa cokali uku sannan ki zuba madarorin turaranki ko wanne cikin kwalbar fiya-fiya
Ki juya sosai ki rufe ya tsumu, wannan garin misik din da ambar din shi zai dinga kara tsuma humra ta dinga kara kamshi za ki iya rufewa kwana bakwai ko zuwa sati biyu ta tsumu.
Comments
Post a Comment