GIRKI ADON UWARGIDA
MIYAR SOYA BEANS
• Waken soya
• Nama
• Kifi banda
• Attaruhu
• Albasa
• Tafarnuwa
• Mai
• Kayan kamshi
Yanda ake hadawa
Dafarko zaki wanke waken ki, kikai a markada miki ki tace kamar za kiyi awara saiki zuba a tukunya ki barshi ya tafasa sannan saiki zuba dan tsami kadan sannan saiki dinga juyawa zakiga yana curewa kamar zai zama awara to saiki sauke ki zuba a kwandon tace taliya ki barshi ya tsane.
Saiki ajiye a gefe ki sulala naman da kayan kamshi da maggi shima sai ki ajiye a gefe shima kifin ki gyara shi ki wanke shi da ruwan zafi ki ajiye saiki daura tukunya ki soya mai sannan ki zuba kayan miya kisa maggi da kayan kamshi.
Idan ya soyu sai ki kawo naman nan da kifin ki zuba da dan ruwa kadan wasu suna amfani da ruwan sulalen nama saiki dan rufe kamar 3min ruwan ya tsane sannan ki kawo wannan soya beans din naki da kika ajiye ki zuba akai ki juya sosai saiki kara rufewa kamar 5min saiki sauke shikenan miya ta hadu.
Comments
Post a Comment