GYARAN BRST
Nono babbar kadara ne kuma kyawunsu yana kara miki kyau da kima gurin miji idan sun lalace kuma ke da kanki baki son ganinsu balle mijinki saboda haka dole ki dinga kula dasu.
Alwai hanyoyi da dama na kula da lafiyar nono, ga wasu daga cikinsu:
Karin girma da rashin faduwa:
Kayan hadi:
- Farar shinkafa
- Garin Alkama
- Garin habbatus sauda
- Garin Ayaba (Plantain).
- Gyada mai malfa (mai zabo)
- Aya
- Madarar gari.
- Zuma
Za a bare bayan plantain sai a yanka shi, a shanya ya bushe, sai a daka, a hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sai a hada aya da gyadar a markada a tace ruwan.
Bayan nan, sai a dora kan wuta a zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da muka hade a guri daya, sai kuma ku zuba garin madara da zuma, ku dama ya yi kauri sai a rika sha safe da yamma.
Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, in kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya sosai, ki rika sakawa. Ki yi haka na tsawon sati biyu, da yardar Allah.
Comments
Post a Comment