Jerin abinci da yake karawa mata masu shayarwa ruwan nono:
Abun da yafi muhimmanci wajen samar da nono mai yawa da inganci ga mace mai shayarwa ita ce irin abincin da macen ke ci.
Yana da muhimmanci mace mai shayarwa ta rika shan ruwa mai tsafta da abinci mai ruwa-ruwa kamar Shayi da madara, kunu da sauransu.
Ga dai jerin abincin kamar haka:-
1- Hatsi:-
Hatsi yana samar da ruwan nono ga mace Mai shayarwa saboda tana samar mata sinadaran vitamin E, B6 da B5 manganese, selenium da sauran su. Baya ga haɓaka samar da ruwan nono, yana inganta lafiyar garkuwar jikin yaro.
2- Alkama:-
Alkama wadda a turance ake kira Oatmeal tana da sinadarai masu gina jiki kuma ga saukin sarrafawa. Mai jego tana iya sarrafa alkama da madara ko da gyada domin kara dandano. Yana samar da ruwan nono sosai.
3- Alayyahu:-
Alayyahu yana daga cikin manyan manyan abinci dake karawa uwa ruwan nono. Hakanan suna da wadata a cikin abubuwan antioxidant, wanda ke taimakawa tsawan lokacin shayarwa.
4- Shinkafa ta gida:-
Yana da kyau mai jego ta dena amfani da shinkafar da aka sarrafa ta a kasashen waje wanda muka fi sani da shinkafar gwamnati ta koma amfani da tamu shinkafar ta gida saboda ita ke dauke da sinadirai da take taimakawa wajen inganta ruwan nono.
5- Karas
Idan mai jego na fama da karancin ruwan nono sai ta dage wajen cin karas ko kuma saka shi cikin abinci ko miya. Karas na dauke da sinadarin vitaman A da wasu sinadaren da ke taimakawa wajen kara yawa da ingancin ruwan nono.
6- Tafarnuwa:-
Baya ga yana dauke da sinadarai masu amfani da yawa. A gefe guda, yana ƙara samar da nono da ma yana kare jariri daga abin mamakin ciki. Mace za ta iya ci haka ko anika shi a cikin abinci.
7- Dankalin Hausa:-
Dankalin hausa yana dauke da sinadarin potassium da kuma carbohydrate da ke matukar taimakawa wajen kara inganci ruwan nono da kuma magance kasala. Ana iya dafa dankalin a ci da miya ko a sarrafa ta wata hanyar.
8- Nonon Saniya:-
Madarar shanu na daya daga cikin abincin da ke kara yawa da ingancin nono ga mai jego. Baya na nonon sauran ababen da ake fitarwa daga nonon kamar kindirmo da man shanu ko Yoghurt duk suna taimakawa suma.
9- Kunu:-
Kunu yana daya daga cikin abincin iyaye da kakanni ke bawa mai jego ta sha da zarar ta fara shayar da jaririn da ta haifa musamman a kasar Hausa. Ana iya sarrafa shi da gero ko masara a bawa mai jego.
10- Hulba:-
A debi garin hulba babban cokali 1 a ruwa kofi 1 a tafasa asa madara a sha.
Comments
Post a Comment