Yadda Ake Hadin Garin Bawon Kankana Don Karin Ni'ima
Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Garin kankana
* Garin kanunfari
* Garin habbatus sauda
* Zuma
Bayani; Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki gauraya ki zuba a cikin Zuma idan ya jiku sai ki dunga sha.
Yadda Ake Hadin Garin Habbatur Rashad Don Karin Ni'ima
Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Garin habbatur rashad
* Garin kistul hindi
* Garin minannas
* Zuma
Bayani; Zaki samu garin habbatur rashad dinki ki hadeta da garin kistul Hindi da garin minannas ki tafasa sai ki tace ruwan ki kawo zumanki ki zuba sai ki juya ki dunga sha.
Comments
Post a Comment