Main menu

Pages

KO KUN SAN AMFANIN DA SOBO KEYI, DA KUMA ILLAR SA GA MAI CIKI?

 



Shan Zobo Yana Maganin Hawan Jini

 Wani masani a fannin karatu na alfanun da ke cikin kayan abinci, Dr Ochuko Erukainure ya bayyana cewa yawaita shan zobo na taimakawa wajen rage illar hawan jini a jikin dan adam a sakamakon sinadaran da ke cikin sa.


Erukainure, wanda babban jami’in bincike ne a ma’aikatar bincike akan masana’antu na gwamnatin tarayya shi ya bayyana haka ga kamfanin dillanci labarai na Nijeriya NAN a jahar Lagos.

A fadarsa, zobo ya na dauke da sinadarin rage ‘Cholesterol’ da ciwon suga da kuma cushewar hanji.


Ya kara da cewa shan kofi daya na zobo bayan cin abinci ya na taimakawa wajen rage kiba mara kyau. Haka kuma ya ce yana taimakawa wajen magance mura da sanyi.

Sai dai kuma masanin ya bayarda shawarar kar a na kara sikari a cikin zobon domin a ci moriyar sinadaran na sa.

Ha ka kuma ya ce mata masu juna biyu su guji shan zobo, domin zai iya haifar da zubewar ciki.


Comments