MAGANIN CIWON MARA LOKACIN AL'ADAH (MENSTRUATION PAIN)
Ciwon mara lokacin Al'adah, abu ne da yake damun Mata da yawa. Amma wasu da zaran sunyi aure to su kan nemi wannan matsalar su rasa, yayin da wasu kuma matsalar jinnu ce ke haddasa musu hakan, kuma yakan kai ga rashin samun haihuwa.
Ko ma dai mene ne ga wasu magunguna nan ku jarraba. In sha Allahu za'a samu mafita.
(1) A samu Tsohuwar Tsamiya a jika a ruwa tare da bushashiyar gauta a rika shan ruwan tun kwana biyu kafin zuwan haila, har lokacin da hailar za ta fara zuba. Wannan maganin Mata da dama sun jarraba kuma sun samu dacewa.
(2) MAN ZAITUN : A karanta ayoyin Alqur'ani a cikin sa sannan mace ta rika shan cokali guda safe da yamma kullum har zuwa lokacin zuwan Jinin al'adar ta ta. Kuma za ta rika shafawa a jikin ta har zuwa marar ta (Amma banda al'aurar ta saboda ayoyin da aka tofa a ciki.)
Shima wannan idan anyi shi za'a dace. Ko da Aljanu ne suke rike mata marar ko suke sanya mata ciwon jikin to za ta samu waraka in sha Allah.
(3) KUSDUL HINDI : Idan an jika shi da ruwa ana shan sa safe da yamma shima yakan magance matsalar ciwon mara ko rashin zuwan jinin sosai, ko kuma rikicewar jinin Al'adah.
(2) A samu man Habbatussauda dan Saudiyyah ko dan Egypt ko Sudan ko Pakistan ko kuma mai kyau, sannan man Zaitun shima mai kyau da turaren Al-Misk (Ja), in zai yiwu a samu garin Hiltit (wanda wasu ke kira da Hantiti) sai a hada su waje guda a rika shafawa a marar. Ba wai sai lokacin Al'adah ba, sannan kuma yana da kyau a dauki tsawon lokaci ana yin sa.
Wannan hadin mujarrab ne ( wato mata da dama sunyi amfani da shi kuma sun samu sauki da izinin Allah ).
Wannan magani yana da karfin da ba ko wace mace ke Iya amfani da shi ba saboda karfin sa, wannan kuwa ba ya rasa nasaba da kasancewar watakila suna da jinnu a tare da su, domin jinnu ba sa son warin wani daga cikin mahadin (wato Al-Misk). Amma in aka daure wajen yin amfani da shi to za a samu waraka biyu da taimakon Allah ( ta ciwon marar da kuma matsalar jinnu din).
_Kuma koda ajiyar Aljanu ne a marar mace ko mahaifar ta, in sha Allahu za ta samu waraka.
Allah ta'ala yasa mu dace
Comments
Post a Comment