Wata Sabuwa!!!..., Kashe Ahmad S Nuhu akai Ba Mutuwar Allah ba, Cewar Safiya Musa.
'Yan magana sukace wai ana dara ga dare yayi. Kowa dai yasan shaharren Dan wasan Hausan nan wato Ahmad S Nuhu, Mijin Hafsat Shehu. Wanda a yau ya Kai kusan Shekara goma Sha biyar a qasa.
To duk tsawon lokacin nan ba a ji wani abu game da mutuwarsa ba sai a yanzu da Safiya Musa tsohuwar Jaruma da tayi tashe a wancan zamanin ta fito a live TikTok dinta take bada labarin cewa kashe Ahmad akayi.
A cikin firan nata tace "har dani aka so a kashe Allah ne Ya tsareni, a lokacin da yanzu nima na mutu ko in sha wahala"
Abin da ya faru dai kamar yadda take bada labarin shine, an kirasu suje gala a Maiduguri, inda tace aka kawo masu manyan kudaden, Ahmad aka bashi N500k ita Kuma 700k, ganin yawan kudin yasa ta dauki 20k kawai tace bata Zuwa.
Bayan Ahmad ya tafi sai ga sakon mutuwarsa, wanda hakan bai bata mamaki ba a cewarta.
Safiya tayi addu'ar Allah Ya tarwatsa industry, ko Kuma Allah Ya kawo wasu tsiraru da zasu gyara ta.
A lokacin da Safiya ke wannan bayani ana ta kiranta daga wurare daban daban don ta daina wannan maganar Amma fa duk da haka sai da takai aya.
To abin tambaya anan shine, me yasa Safiya tayi shiru duk tsawon lokacin nan bata fadi maganar ba sai yanzu, Kuma me yasa bata yi kokari hana Ahmad yin tafiyar ba?
To amna dai ance gani da Ido yafi, ku Kalli video inda take bayanin.
Comments
Post a Comment