SARKIN MACHINA TARE DA ƊAN UWAN SA MACIJI
Kamar dai yadda aka sani an haifi sarkin Machina dake jihar Yobe na wancen ƙarni a tare da Machiji, hakan yasa machizai basa yiwa jama'a komai garin Machina
Jama'a da dama har daga ƙasashen waje suna ziyartar garin Machina dake jihar Yobe domin buɗe ido harma da gidajen jaridu
Tarihi ya nuna cewar a wasu shekaru da su ka wuce, matar sarkin Machina ta haifi'yan tagwaye, mutum da maciji
- An ce wannan shine dalilin da ya sa har yanzu macizai ke da daraja a garin Machina domin ba a kashe su, kasancewar ana yi ma su kallon jinin sarauta
- Mazauna garin Machina sun yi imanin cewar macijin da aka haifa tare da sarkin garin ne ya haifi macizan da ake gani na shawagi a fadar sarki da kewaye Duk da kasancewar jama'a da dama na ganin maciji a matsayin abin tsoro, sai ga shi a garin Machina da ke jihar Yobe macizai sun zama 'yan gida don kuwa har gaisuwa su ke kaiwa sarkin garin a fadar sa.
Ga dukkan wanda Allah ya bashi ikon ziyartar garin Machina zai sha mamaki
Ga dai sarki da ƴan'uwansa Machizai a fada abinsu
Comments
Post a Comment