Main menu

Pages

WANI MUHIMMIN SIRRI NA XENDER DA BA KOWA YA SANI BA




 ANFANIN XENDER DA MUTANE DA YAWA BA SU SANI BA:


Da yawa mutane suna da Xender, amma ba su san yana wannan aikin ba! Wanne aiki? Sau da yawa za ka ga video da ka ke so a Facebook amma sai ka rasa yadda za ka yi ka same shi. To ba dole sai ka bukaci wanda ya dora video din ya tura maka ba, da Xender din ka za ka sauke shi a kan wayar ka kamar haka: (Ka dubi hotunan, ka bi su daga number 1 zuwa 6, ko kuma wannan rubutun don saukakewa):


1. Ka yi copy na link din post din da aka saka video din (kamar yadda aka nuna arrow na wajen kofan link a hoto)


2. Sai ka bude Xender din ka ka je kasan Xender din akwai inda a ka rubuta 'Social' (an nuna wajen a hoto).


3. Sai ka danna kan 'Social' din zai kai ka wani waje da aka rubutu 'Paste&Downdload'.


4. Sai ka danna kan 'Past&Download' zai yi paste na link din da ka kwafo. Yana yin paste za ka ga video din ya bayyana. (Kamar yadda ya ke a hoto).


5. Shi kenan sai ka je kan Gallery na wayar ka za ka samu video din a can.


Comments