YADDA AKE HADA TURARE.
Turare mai kamshin dadi, maisuna ruda maigida
Kayan hadi
・ halud kg3 sendal kg 1
・ hawi kg half
・ farcen gwangwanin tumatir
・ miski cokali 4
・ sarki turaren babba 1
・ binta saddan babba 1
・ hafsa 1
・ bokur 1
❒ kafi kafi
❒ assasarubiya 1
❒ oassion 1
❒ massarubiya 1
☐ ledus sahi 1
☐ Onte man shw 1
☐ sanyin turaren cheri 1
Karamin sandal 1 madarar turaren ambarda farko zaki dora farce a wuta da ruwa. Idan ya tafasa na tsawon minti 30 saiki wanke da omo da soson waya idan ya wanku saiki baza ya bushe saiki daka shi sama sama sannan ki dora tukunya awuta ki zuba suga gwangwani 2 da ruwa cokali 8 idan ya narke yayi ja ya tsinke yayi tsululu saiki zuba halud.
Da hawi da sandal kici gaba da jujjuyashi sosai.idan yasoyu da ruwan suga saiki juye acikin babbar kwano.kibari yayi minti 20 sannan ki daka miski kar yayi danshi sosai ki zuba ki daka jawi shima kar yayi danshi sosai.
Ki zuba saiki zuba madarar turaren duka ki zuba farce shimaki jajjagashi ki rufe tsawon awa 48 sannan kizuba a kwalba ko roba. Duk inda kinka wuce ko kika zauna saikin bar kamshi. Koda yaushe dakinki cikin kamshi. duk wayannan abubuwan dana lissafa za'a iya samun su duk inda ake sayar da magungunan Musulunci
Comments
Post a Comment