MIYAR KIFI
Yadda ake yin miyar kifi ba tare da kifin ya farfashe ba.
Ingredients
-- Kifi sukumbiya
-- Tattasai
-- Attaruhu
-- Cabbage
-- Albasa
-- Curry
-- Maggi
-- Man ja ko Man gyada
Preparation
Zaki wanke kifinki da lemon tsami ko toka domin fidda qarninsa da kuma yaukin dake jikinsa sai ki yanyanka amma sai kinyi sauri domin idan kankarar jikinsa ta narke zai iya dagargaje miki wajen aikinsa,
sai ki barshi yasha iska domin ya tsane, in ya tsane sai ki barbadeshi da maggie ki jerashi a farantin gashi kisa shi a oven idan kuma baki da oven din sai ki soyashi a mai amma karki yawaita juyashi gudun dagargajewa.
Idan yayi sai ki aje ki dauko attarugu da albasa tattasai da cabbage da kika yanyanka kika wanke ki dora kasko a wuta Kisa mai ki soyasu kisa maggie da curry idan sun fara hadewa jikinsu sai ki dan sa ruwa a ciki,
sannan ki kawo kifin kisa a ciki yayi Kaman 10 minutes saiki sauke, kisa mai ki soyasu kisa maggi da curry idan sun fara hade jikinsu sai ki dan sa ruwa a ciki, sannan ki kawo kifin kisa a ciki yayi kaman 10 minutes saiki sauke.
HANYA TA BIYU KUMA ITA CE!
Hanya ta biyu da za a bi Kuma shine, Zaki yayyanka kfinki ki samu ruwan dumi, ki Saka kifin a ciki ki wanke shi tas da Wannan jini jinin, sai ki tsame shi ki doddorashi a Dan kwando inda ruwan zai tsane.
Sannan ki koma wajen hada miyar ki sai kin tsaida ruwan miya shi Kuma kifinki ya tsane sai ki dakko shi ki sassaka a cikin miyar. In kkai haka Insha Allah ba zai dagargaje ba.
Comments
Post a Comment