YANDA AKE SHAWARMA..
Ana siyarda shawarma bread a super market,
in kuma baki san inda zaki samu ba, ga yanda zaki hada naki..
Kayan hadi.
-- Flour
-- Gishiri kadan
-- Sugar kadan
-- Yeast kadan
-- Ruwa...
Yanda Zaki hada
Ki kwabasu waje daya, yayi kamar kwabin cincin..ki barshi yayi kamar minti 20 sai ki samu paranti da kwalba koh rolling pin ki yanka kwabin kadan ki murzashi yayi fale fale amma ba sosai ba, ki tabatar flour yayi circle in kina murzawa kar ya zamana baida shape. sai ki dauko non-stick frying pan, in kuma baki dashi, zaki iya anfani da murfin tukunyan gargajiya mai kafa 3 nan, saiki daura akan wuta, amma ya zamana wutan kadan ne don kar biredin ya kon, saiki dauko flour da kika riga kika murza ki saka akan non-stick din koh murfin tukunya.
Yayi kaman 2minutes, sai ki juya dayan gefen shiya yayi 2minutes saiki cire ki saka acikin leda ki rufe, haka zaki tayi har sai flour din ya kare, ba dole bane sai kin shafa mai akan non-stick din koh murfin tukunya ba, amma in kina so zaki iya shafa dan kadan.
Bayan Nan Kuma saura me?
Sai muzo kan kayan hadin cikin shawarma din.
1. Bama(mayonnaise)
2. Gashashen/tafasasshen kaza, amma zaki iya anfani da nama/kifi
3. Yankaken Cabbage
4. Yankaken green pepper
5. Sugar da gishiri kadan
6. Zaki iya anfani da duk kayan hadin da kikeso aciki amma yaza mana kin saka abubuwan da na lisafa asama..zaki iya hada duk kayan hadin waje daya ki chakuda sai ki dauko flour da kika gasa/shawarma bread,
Sai ki debo kayan hadin ki saka a farkon flour din sai kiyi mai nadin tabarma, koh kuma zaki dauko gashasshen flour ki shafa mashi bama(mayonaise) a koh ina, sai ki dibo cabbage dinki ki jerashi daga farkon flour din, sai ki dauko kazanki shima ki sakashi akan cabbage da kika jera da sauran kayan hadin, sai kiyi mishi nadin tabarma.
Don kada nadin ya kwance zaki iya soka mishi toothpick guda 2 sama da kasa, koh kuma ki daura non-stick akan wuta saiki dauko flour ki da kika riga kika saka kayan hadin aciki ki daura akan wuta ya zamana bakin da yake abude zaki kwantar acikin tukunyan yayi kaman 2 minutes, zaki ga bakin zaikama.
Comments
Post a Comment