Azumi Cikin Tsananin Zafi
Daga cikin abubuwan da za su ɗauke wa mumini jin wahalar azumi a cikin wannan yanayi na zafi, abubuwa ne guda biyar:
Na ɗaya, Tunawa da yawan ladan da mutum zai samu idan ya tsarkake niyyarsa.
Wata baiwar Allah daga cikin magabata na kwarai ta yi tuntube sai farcenta ya fita, sai aka ga ta yi dariya, tana cewa: "Dadin ladansa ne ya mantar da ni zafin ciwonsa".
Na biyu, Tuna azabar wutar jahannama da Allah ya yi wa masu laifi alkwarin shigar ta, domin tsananin zafi yana daga cikin hucin wutar jahannama, kamar yadda ya zo a hadisin Abu Huraira (RA). [Duba, Bukhari#3260 da Muslim#617].
Na uku, tuna girman wanda ya yi umarni da yin azumi, da tuna ranar tsayuwa a gabansa. Wannan zai rage wa bawa jin duk wata wahala ta yanayin zafin rana.
Na huɗu, halarto da cewa, Allah (SAW) yana ganin bawansa lokacin da yake tsaka da wannan bautar ta azumi, yana sane da duk irin wahalhalun da yake sha. Duk wanda ya sakankance da cewa, masoyinsa yana ganin irin wahalar da yake ciki saboda soyayyarsa, to wahalar takan zo masa da sauki, kamar yadda Allah (SAW) ya yi wa Manzonsa nuni da haka inda yake ce masa: (Ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka don ko lalle kana karkashin lurarmu) [Suratut Dur, aya ta 48].
Na biyar, Nutse wa cikin soyayyar wanda ya yi umarni da yin wannan ibada ta azumi. Duk wanda zuciyarsa ta cika da son Allah (SAW), to zai so abin da yake so komai wahalarsa kuwa.
Allah (SAW) muke roka da ya karbi ayyukanmu ya ba mu cikakken lada a kai. Amin.
Comments
Post a Comment