Main menu

Pages

BANDITS DIN DA SUKA KSI HARIN JIRGIN KASAN ABUJA- KADUNA KARIN FARKO SUN FITO SUN YI JAWABI.

 


karon farko, 'yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasan fasinja da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun yi jawabi, inda suka yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matuƙar gwamnatin Najeriya ba ta biya musu buƙatunsu ba.


A jiya ne, wani bidiyo da ya bayyana, ya nuna wasu daga cikin maharan ɗauke da bindigogi suna iƙirarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ƙasan a ranar Litinin din makon jiya.


Bidiyon, wanda bai kai tsawon minti 1:30 ba, ya nuna huɗu cikin 'yan bindigar sanye da kakin sojoji, rufe da fuskoki a tsaye suna iƙirarin ci gaba da riƙe fasinjojin jirgin ƙasa da suka sace a ƙarshen watan jiya.


Ba a dai ga fasinjojin a cikin taƙaitaccen bidiyon ba, amma mutanen da suka yi maganar sun tabbatar da cewa suna riƙe da su.


Sun kuma ce ba za su sake su ba har sai gwamnati ta biya musu buƙatunsu, amma ba su bayyana buƙatun nasu ba.



Wani cikin masu jawabin ya ce ba buƙatar kuɗi ce ta sanya su sace fasinjojin ba, suna masu yin iƙirarin cewa gwamnati ta san buƙatun.


Bidiyon ya nuna maharan ne tare da Alwan Ali Hassan, daya daga cikin fasinjojin da aka sace a jikin wata motar igwa da wuta ta cinye ƙurmus, a wani wuri mai bishiyoyi.



An sako video ne da yammacin jiya Laraba, kwana tara bayan wani hari kan jirgin ƙasan fasinja da ke tafiya zuwa Kaduna.


Maharan sun ce sun saki Alwan Hassan ne saboda tausayin tsufa da kuma alfarmar azumin watan Ramadan.


Sai dai wasu kafofin labarai a Nijeriya sun ce sai da aka biya miliyoyin naira kafin sakin nasa.


A cikin bidiyon, an ji Alwan Hassan yana cewa an sake shi ne saboda tsufa amma ya bar wasu mutanen da dama a can.


Ya kuma ce mutanen da ya baro suna cikin buƙatar ɗauki.


Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Nijeriya ta ce fasinja 162 ne suka ɓata bayan harin na ranar Litinin.


Babu tabbaci ko duka wannan adadi ne ke can a hannun maharan.


Bidiyon dai bai yi ƙarin haske a kan ƙungiyar da ta kai harin ba, wadda kwanan baya, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa'i ya ce Boko Haram ce.


An dai ji mai magana na farko cikin 'yan bindigar da suka yi magana a bidiyon na buɗe jawabi da wasu kalamai na Larabci, kafin ya ƙarƙare da hamdala.

Comments