Matslar Tsaro A Nigeria El RUFA'I Ya Koka
Idan gwamnatin tarayya ta gaza kawo karshen ta’addanci za mu yi gaban kan mu mu yo hayan askarawa daga waje su gama da su – El-Rufai
Ba ni da ra’ayin takarar shugaban kasa, lokacin da aka zabe ni gwamnan Kaduna gashin kai na baki wul yanzu duk furfura – El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyanawa manema labarai a fadar shugaban Kasa cewa ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayanin halin da ake ciki game da matsalar tsaro a kasar nan musamman a jihar Kaduna.
Kamar yadda Daily Trust ta buga, El-Rufai ya ce abin ya wuce gona da iri yanzu, ƴan bindiga na cin karen su ba babbaka. Sai su afka duk inda suke so, su aiwatar da ta’addancin su babu fargaba ko tsoron jami’an tsaron kasar nan.
” A shirye suka kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna, sun san wani tarago za su shiga da waɗanda za su sace. A shirye suke
” Na daɗe ina faɗin cewa lokaci yayi da za a nausa cikin dazukan da waɗannan ƴan bindigan suke ɓoye a yi musu ruwan bamabamai, a kashe su.
” Idan ba haka a ka yi ba, toh ina tabbatar muku cewa ba za a zauna lafiya a kasar nan ba domin za su iya tarwatsa kasar ma baki ɗaya.
Mutanen suna samun kuɗi na fitan hankali. Ba su tsoron gwamnati da sojoji. Ba su bane a gaban su. Menene ya sa ba za a bi su can cikin dajin ba a fatattaka su gabaɗayan su.
” An san inda suke. SSS na bayar da rahoton halinda suke ciki kullum amma babu abinda ake yi a kai.
A karshe ya ce shugaba Buhari ya bashi tabbacin cewa lallai gwamnati za ta ɗauki mataki don ganin an kawo karshen hare-haren ta’addanci a kasar nan.
” Mu dai idan abin ya gagara, za mu ɗauko askarwan haya daga waje su zo su gama mana da su. Shike nan kowa ya huta, idan abin ya gagari sojojin Najeriya.
A kullum tunani na shine tsayawa a gaban Allah ran gobe kiyama – El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tsananin rashin tsaro da ya addabi ƴan Kaduna da Najeriya na ci masa tuwa a kwarya matuka da a kullum tunanin sa shine gamuwar sa da Allah, me za su ce a matsayin su na shugabanni.
Gwamna El-Rufai ya faɗi haka ne a ziyarar jaje da ta’aziyya da ya kai wa mutanen yankin Giwa da ke fama da hare haren ƴan ta’adda babu ƙakkautawa a ƴan kwanakin nan.
Comments
Post a Comment