Main menu

Pages

KO KUNSAN WANNAN SIRRIN GAME DA CARROT

 


Amfanin karas ga Fata

Kamar yadda aka sani cewa karas na dauke da sinadarin bitamin A domin gyara ido da ganin mutum, bayan haka, akwai ababe da yawa da karas yake yi domin inganta fata. Domin sanin muhimmancin karas, shi yasa a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da shi domin magance cututtukan fata da dama.


Cin karas na sanya fata sheki da laushi ga kuma gyara ido domin yana dauke da sinadarin bitamin A da wasu sinadaran gyara jiki.


A markada karas a sha ruwansa domin magance tabon fuska da kuma sanya ciwo a fata warkewa da wuri.

Karas na dauke da bitamin A don haka yana taimakawa wajen rage tsufar fata. Don haka a rika yawan markada shi a shafa a fata ko a sha akalla kullum a rana.


Shan jus din karas musamman lokacin zafi na magance tabon rana da yake fesowa a fuska. Sai a ga fuska ta yi dabbare-dabbare launi daban-daban. Yana da kyau a yawaita shan jus dinsa a lokacin zafi.

Rashin cin karas a abinci na janyo gautsin fata don haka, sai a rika shan jus din karas domin samun fata mai sulbi.


Domin sinadaran da karas ke dauke da su, yana taimakawa wajen magance kurajen fuska da sauransu. Fesowar kurajen na faruwa ne idan an rasa sinadarin bitamin A a fata don haka sai a ci karas. Amma yawan cin karas na iya canja launin fata.


Idan an ji ciwo za a iya shafa dakakken karas a wurin domin yana taimakawa wajen warkar da ciwo.

A markada karas sannan a zuba madara da zaitun kadan da kuma zuma sannan a kwaba a shafa a fuska na tsawon minti 30. Hakan na magance fesowar kurajen fuska.

 

Comments