Main menu

Pages

LUKMAN NA FILM DIN LABARINA YA FITO TAKARAN SIYASA A KANO



 Kano – Jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa, Yusuf Saseen, wanda jama’a suka fi sani da Lukman na shirin Labarina Series, ya tsaya takarar siyasa a Kano.


A wani rubutu da abokin Jarumin kuma Darakta a Kannywood, Sulaiman Bello Easy, ya saki a shafinsa na Instgaram, ya nuna Jarumin zai nemi takara ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP. Jaridar legit na ruwaito.



 

A fastar takara da ta karaɗe shafin Instgaram, Lukman Na Labarina, ya tsaya takarar dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Kano Municipal a zaɓen 2023 dake tafe.


Darakta Sani Easy ya ce:


“Duk da ba na siyasar PDP amma dole na yi wa abokina kara na tallata shi saboda ingancinsa da sanin mutuncin al’umma, bana jin ko a wace jam’iyya ya fito zan ƙasa hidimta masa.”


“Duba da gudummuwar da yake bai wa al’umma ta kowane ɓangare, a gaskiya ya cancanta, muna barar kuri’un ku da kuma fatan Nasara.”


Waye Yusuf Saseen?


Ciakkken sunansa shine, Yusuf Muhammad Abdullahi, amma an fi saninsa da Yusuf Saseen, haifaffen jihar Kano ne wanda ya ta so a cikin jihar, ya yi karatun Firamare da Sakandire a Kano.


Fitaccen Jarumin, wanda ya shahara bisa rawar da yake takawa a shirin ‘Labarina mai dogon Zango’ a matsayin ɗaya daga cikin Samarin Sumayya, ɗan asalin Anguwar gini ne ta cikin garin Kano.


Bayan kammala karatun Digirinsa a Jami’ar Bayero, Lukman ya yi aikin bautar ƙasa NYSC a jihar Nasarawa, daga bisani ya shiga harkar shirya fina finai ta Kannywood.



Comments