Abubuwan da Ke sa warin Baki da Yadda za a magance shi
Abubuwan dake kawo matsalar warin baki wanda a likitance aka fi sani da Halitosis suna da yawa, wasu daga cikin su sun hada da;
1.shan taba, shan giya, cin tafarnuwa albasa da sauransu.
2.Rashin tsaftace baki yadda ya kamata.
3.kwayoyin cuta na bacteria da ke cikin baki.
4.Cututttuka kamar diabetes , lung disease, kidney disease, cancer, liver disease, respiratory tract infections,duk suna taimakawa wajen kawo bad breath ko warin baki.
Sauran cututtukan dake taimakawa wajen kawo warin baki sun hada nasal odor,tonsil stones, yeast infections na baki, da kuma gum disease.
Bushewar baki watau dry mouth ko Xerostomia a likitance.
Magani A Likitance
1.wanke baki ta hanyan amfani da Baking powder wannan ya kashe bacteria din dake kawo warin baki.
2.Cin yayan itace dake dauke da fiber kamar apple, ayaba da mangoro.
3.shan blacktea saboda yana dauke da sinadarin polyphenols wanda yake kawar da sulfur compounds da oral bacteria.
4.Yawan tattauna chewing gum ko mints don yana taimakawa wajen hana baki bushewa (dry mouth).
4.Shan vitamins supplements ko abubuwan da ke bada vitamin c kamar yayan itatuwa.
5.Daina shan taba idan anayi.
6.Tsaftace baki a kalla sau biyu a kowacce rana.
Comments
Post a Comment