FARFESUN KABEJI
KAYAN HADI;
1_KABEJI
2_ALBASA
3_NAMA
4_MAGGI, DA GISHIRI
5_MANGYADA
6_JAN TATTASAI
7_KOREN TATTASAI
Yadda za'ahada
Dafarko uwar gida zaki samu kabeji babba mai kyau, sai ki yanke wannan jijiyoyin masu kauri na jiki, sai ki yayyanka ki zuba a ruwa ki wanke shi tas, ki tsame shi a kwandon tace taliya ko salat, kibarshi ya tsane, sai ki dauko albasa ki bare ta ki yanyanka mai kyau akwance itama ki wanke ta ki ajiye daban, saiki dauko koren tattasai da jan tattasai kiyan kasu kanana a aje gefe, in kin ga kina da wadata zaki iya saka karas da green Beans da peas, in babu sai kiyi da tattasan da albasar.Sannan ki tafasa nama da albasa maggi gishiri, citta thyme in kina so, inya tafasu sai ki tsame shi daga ruwan kibarshi yadan tsane, sai ki dauko kaskon suya ki zuba mai in yayi zafi ki yanka albasa, sai ki soya naman amma fa naman bada yawaba ake sakawa ba, kamar yanka goma ko sha biyu kanana,i dan kuma ba halin saka nama sai ki barshi, bayan kin soya naman sai ki tsame shi a cikin man,
Sai ki zuba yankakkun tattasai da albasar nan, ki soya su amma fa ba sosai ba karsu kone, sai ki dauko kabejin ki zuba akai sai ki dauko maggi, kisa seasonings da dan kori, ki zuba akai kijuya sai ki dauko ruwan naman da kika tafasa ki zuba a ciki idan ruwan yayi kadan saiki kara ruwa, sannan ki dauko naman da kika soya ki zuba a ciki ki juya sosai yadda kayan hadin zasu hade jikinsu, sai ki rufe ki rage wuta ki barshi zuwa yan mintuna, sai ki sauke shikenan. Aci Lafiya.
Comments
Post a Comment