Yadda Ake yin yoghurt din waken soya
Abubuwan bukata
Waken soya
Sugar
Filebo (flavour (milk or vanilla))
Yadda ake hadawa
Da farko za ki wanke wakenki, ki cire tsakuwa sai ki jikashi ya kwana da safe ki wanke ki cire dusar za ki wanke kamar za kiyi alale.
Idan kin gama sai ki kai inji a markada miki, kar a markada akan komai ki tabbatar injin an wanke tsaf.
Idan ankawo markaden, sai ki tace kamar za kiyi awara,
Anan sai ki dauko tukunyarki mai kyau ki juye, ki dora a wuta ki tsaya ki kula sosai idan ya tashi tafasa za ki ga yana kumfa kamar ruwan gyada.
Sai ki ta dagashi kina juyawa dan kar ya zuba, idan ya daina kumfa, sai ki barshi ya dahu sosai. In ya yi za ki ga ya yi dan kauri sai ki sauke.
Ki bari ya dan huce ki sa sugar da flavor, ki juyashi sosai, sai ki dandana kiji suga da flavour idan ya yi sai a sha .
Comments
Post a Comment