Yan Najeriya sun fara rububin zuwa ofisoshin hukumar da ke rijistar lambobin wayar hannu da katin dan kasa a fadin kasar.
Wannan ya biyo bayan matakin rufe layukan wadanda ba su yi rajistar layukansu ba da katinsu na dan kasa.
A ranar 4 ga watan Afrilu, hukumar da ke kula da sadarwa ta kasa, Nigerian Communication Commission (NCC) ta fitar da wata sanarwa da ke umartar kamfanonin sadarwar kasar da su hana dukkan layukan da ba a yi ma rajista ba kiran wasu layukan.
Ba tare da bata lokaci ba kamfanonin sadarwan suka dauki matakin da aka umarce su dauka.
Daga nan ne 'yan Najeriyan da basu yi rajistar layukansu ba suka fara fuskantar matsaloli saboda ba sa iya kiran kowa da layukan nasu.
Me ke haifar da matsalar rashin kammala rijistar layukan?
Tun bayan da aka fara aiwatar da matakin, layukan 'yan Najeriya fiye da miliyan 75 sun daina aiki, kamar yadda kamfanonin sadarwan suka sanar.
Sai dai matakin ya shafi mutanen da ke cewa tuni suka yi rajistar layukansu na waya amma ba sa iya kiran wayoyi domin hanin ya shafe su.
Kuma a hukumance ana bukatar duk wanda ya hada layukansa da katin dan kasa ya karbi tabbacin rajistar ta yiwu daga kamfanin sadarwan da ya sayar ma sa da layin tun da farko.
Amma wasu mutane sun yi ikirari cewa duk da cewa sun kammala rajistar, har zuwa wannan lokacin ba su sami sakon tabbatar da rajistar ta kammalu ba, wasunsu kuma sun ce sun sami sakon amma an dode layukan nasu.
Wani babban jami'in daya daga cikin kamfanonin sadarwa ya bayyana dalilan da ka iya hana rajistar lambar wayar da mutum yayi ya ci karo da cikas.
Ga jerin bayanan da ya sanar da mu:
- Yana yiwuwa ba a kamamla rijistar ne ba
- Kuskure daga na'ura mai kwakwalwa na iya samar da matsalar
- Yana yiwuwa an hada lambar zama dan kasa da layukan waya da suka cika yawa
- Rashin iya hada layukan wuri guda daga hukumar NIMC
- Yankewar sabis
Ga abin da ya dace ka yi idan aka dakatar da layinka bayan ka hada shi da katinka na dan kasa
Babban jami'in sadarwan ya ce akwai mafita ga dukkan wadanda wannan matakin ya shafa, kuma na farko shi ne ya zityarci ofishin kamfanin sadarwar da ya sayar masa da layinsa.
Ya kuma ce kamfanonin sadarwa ba sa son dakatar da layukan wayarsu, saboda yana shafar ribar da suke samu.
Kuma ya ce kamfanonin na bukatar karin abokan hulda ne ba raguwarsu ba.
Murtala Mohammed shi ne shugaban reshen hukumar da ke rajistar dan kasa a ofishinta na Masallacin Murtala a Kano ya tabbatar da wannan shawarar da babban jami'in sadarwan ya bayar a sama:
"Idan suka hana ka kiran wasu lambobi, sai ka tafi ofishinsu domin mika kokenka. Kamfanin sadarwan zai ba ka wasikar da za ka kai wa hukumar NIMC domin su warware matsalar daga bangarenta.
Abubuwan da ake bukata domin yin rijistar wayar hannu da lambar dan kasa
Bayan ka yi rajistar layinka na waya da katinka na dan kasa, za ka bukaci:
Lambarka ta wayar salula
Cikakken sunanka da na mahaifinka
Lambarka ta dan kasa (NIN), kana iya gano ta ta hanyar latsa *346# a tarhonka
Adireshinka na imel
Kwanan watan da aka haife ka
Yadda ake hada lambar MTN da lambar dan kasa ta NIN
Ka ziyarci shafin intanet na MTN da ke ba ka damar yin rajistar a https://mtnonline.com/nin/
Za ka ga wani fom da za ka cika da cikakken sunanka
Sai ka saka lambarka ta MTN
Sai ka shigar da lambarka ta dan kasa wato NIN
Sannan sai ka shigar da adireshinka na imel
A karshe sai ka aika da komai ta hanyar latsa wurin da aka rubuta kalmar 'SUBMIT'.
Kana kuma iya latsa wadannan lambobin daga layinka na MTN, *785#
Za a bukaci ka shigar da lambarka ta dan kasa wato NIN mai lambobi 11, sannan sai ka tura shi. Zai sanar da kai cewa sakon ya isa.
Bayan kwanakin da aka diba sun kare kuma layinka na waya ba a hada shi da lambar dan kasa ta NIN ba, ga abin da ya kamata ka yi...
Yadda ake hada lambar GLO da lambar dan kasa ta NIN
Da farko za ka aika da sakon tes, wanda a ciki za ka rubuta kalmar 'Update NIN', (sai ka bar sarari) NIN (sai ka bar sarari) Sunanka (sai ka bar sarari) Sunan mahaifinka sai ka tura su ga 109.
Yadda ake hada lambar Airtel da lambar dan kasa ta NIN
Da fari sai ka latsa wadannan lambobin daga layinka na Airtel - *121*1#
Sai ka shigar da lambobinka 11 na dan kasa
Za ka ga wani sakon tes da ke sanar da kai cewa komai ya yi.
Yadda ake hada lambar 9mobile da lambar dan kasa ta NIN
Da farko sai ka ziyarci wannan shafin na intanet - https://9mobile.com.ng/nin
Sai ka latsa wani koren wuri inda aka rubuta 'verify and link your NIN now'
Ma'aikatar Sadarwa ta Najeriya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su daina cajin abokan huldarsu naira 20 bayan sun nemi a sanar da su lambarsu ta NIN, kuma hanin ya fara aiki nan take.
Saboda haka kowa na iya binciko lambarsa ta dan kasa ta hanyar aikawa da *346# kyauta
Allah Yasa a dace Ameen.
Comments
Post a Comment