Main menu

Pages

ABUBUWAN DA YA KMT KU LURA DASU IDAN ZAKU SAYI WAYAR ANDROID




 Duk wanda zai sayi sabuwar waya kirar android to ya lura da wadannan abubuwan


Akwai abubuwa da yawa daya kamata idan mutum zai sayi wayar hannu kirar android (Smartphone) ya lura dasu kuma yayi tunanin a kansu kafin ya saya.



Kowa dai ya sani mutum bazai so sayan waya ba kuma daga ya saya ya sayar saboda wasu abubuwa da basuyi masa ba kuma baiyi tunaninsu ba lokacin da zai sayi wayar, har saida ya saya tukunna yaga wayar bata zo da wadannan abubuwan ba, ko bata masa yadda yake so a kuma lokacinda yake da bukatar hakan.



Wani sai kuga ya sayi sabuwar waya amma photo ma saidai ya karbi wayar abokinsa ya dauka saboda tasa bata da camera mai haske da dai sauran abubuwa, dan haka muka kawo muku wasu daga cikin abubuwan da ya kamata duk wani wanda zai sayi waya kirar android daya lura dasu kafin ya saya domin zasu taimaka masa wajen sayen waya mai kyau, kuma wacce zaiji dadin amfani da ita.



Abubuwan daya kamata ku lura dasu idan zaku sayi sabuwar waya sune;


1 Battery

Na farko kenan daga cikin abinda zaku fara lura dashi kafin sayen sabuwar waya shine battery, domin yana taka rawar gani wajen sanyawa mutum yaji yana son wayarsa idan har battery dinta mai kyau ne, haka zalika duk wayar da bata da battery ko bashi da karfin rike charge, to duk kyawun waya tana fita a ran mai ita ko kuma mai amfani da ita.


Dan haka idan mutum zai sayi sabuwar waya to yana da kyau ya lura sosai da girman battery dinta.



2. Memory :- Waya tana da memory guda biyu, random access memory (RAM) da kuma read only memory (ROM). Shi RAM memory ne dake kula da aikin waya kamar saurin gabatar da abubuwa da kuma nisan abu. Haka kuma shi ROM ya ta'allaka ne ga wata ma'ajiya ta adana wakoki da videos da photos da sauran abubuwa kamar Apps da dai sauransu.


Ana bukatar mutum idan zai sayi waya to yayi duba ga memory dinta duka guda biyun, domin wani yana da bukatar waya wacce zatai masa aiki ko browsing da sauri sannan yana da bukatar ajiye abubuwa akan wayar, dan haka idan mutum ya sayi waya mai karamin memory baza tai masa duk wadannan abubuwan ba.


Dan haka idan mutum zai sayi waya to ya lura sosai da girman memory dinta, domin yanzu hatta Apps akwai wadanda baza su zauna akan waya ba idan har memory dinta karami ne.


3 Camera :- Yanzu wani lokaci muka shigo na daukar photo ko yin video da wayoyin hannunmu domin mu dora akan sauran social media platform din da muke dasu kamar WhatsApp, Facebook, Tik tok, wanda kuma idan za muyi photon ko bidiyon muna da bukatar suyi kyau sosai domin su birgemu kuma su birge jama'a, dan haka ya zama dole idan mutum zai sayi waya to ya duba kala da girman camera dinta, kada ya sayi waya kuma yaje baza ta iya dauka masa photunan da yake so ba karshe ma sai yaje yana aron waya a gurin abokansa.


4 Kudin wayar (Price) :- Wani lokacin mutane suna son sayan abu da sauki kuma sai suce mai kyau suke so, wannan kuma kamar yanada wuya mutum ya samu abu mai kyau kuma mai sauki, dan haka duk lokacinda mutum yake son sayan waya mai kyau data tara wadannan abubuwan dole saiya kawar da kansa domin za tayi tsada koda kuwa ba sosai bane.


Tunda shi abu mai kyau dole zaiyi tsada, dan haka idan har mutum yana son sayan waya to ya tara kudi wanda zai ishe shi sayan wacce yake so, duk da cewa akwai waya masu saukin kudi kuma masu kyau.

Comments