BATANCI GA ANNABI: "Muddin Hakan Ya Tabbata To Ba'a Kama Wanda Ake Zargi Da Aikata Laifi", Barr. Aysha Ahmad Mohammad
Daga Barr. Aysha Ahmad Mohammad
Wata ƙwararriyar Barista a Kaduna tayi sharhi kan abinda ya faru a Sokoto kuma ga yadda sharhin nata wanda ta sanya a shafinta na Facebook ke cewa: "Abinda ya faru a Sokoto abune da duk wani musulmi zaiyi Allah wadai dashi. Babu wani musulmi dake aibata addinin Kirista ko kuma Malamansu a iya sanina.
Amma a wani bangaren ba haka bane. A koda yaushe burin masu yin addinin da ba musulunci ba, shi ne aibata musulunci da Annabi Muhammad SAW, wanda ko a ina ansan yadda cin zarafi ko aibata shi yakan tunzura Musulmi a duk inda yake."
"Abinda ya faru a sokoto, Akwai abinda ake kira da “defense of provocation” a criminal law wanda muddin ya tabbata to ba'a kama wanda ake zargi da aikata laifi kamar yadda ya faru a wannan case ɗin",
Lauyar ta cigaba da cewa "Akwai abinda ake kira da “defense of provocation” a criminal law wanda muddin ya tabbata to baa kama wanda ake zargi da aikata laifi kamar yadda ya gudana a wannan case din. Saboda daga lokacin da ta aika da audio din Wazup group dinsu da kuma lokacin da aka aikata abinda aka aikata a akanta yana cikin ya nayin da defense of provocation zai yi tasiri akan wadanda ake tuhuma."
"Zaiyi kyau Gwamnati ta tsawata iya tsawatawa akan aibata Addinin mutane, Manzannin su, Annabawan su da kuma Malamansu don kuwa babu wanda zai iya jure ko hakurin aibantamai abin bautarsa ko ibadarsa." inji ta
Allah ƙarawa Annabinmu daraja S.A.W
Comments
Post a Comment