Applications guda 3 da Google ta Hana amfani da su
Google ya cire wasu Apps guda uku daga Play Store dinta, wadannan apps an gano cewa indai kayi installing dinsu a wayarka to kuwa suna sace ma kudi ne a boye baka sani ba ta hanyar yin sign up zasu sanya ma yin subscription da kudi masu yawa, wanda a shekara zaka ga yawan kudin sunkai pounds masu yawa.
Google Play Store apps ta cire Style Message, Blood Pressure App da Kuma Camera PDF Scanner, wadannan duk kansu an gano cewa akwai malware joker a boye a jikinsu bayan binciken da akayi.
Yanzu dai already wadannan apps guda uku an ciresu daga Google play Store, idan kayi downloading daya daga cikinsu ko ma dukkan su to kayi gaggawar ciresu daga wayarka ta Android.
Bari mu kara rubuta maku sunan nasu ajere don ku kiyayesu
- Style Message
(com.styleacat.mesagearound),
- Blood Pressure App
(blood.maoding.raise.bloodrate.monitorapp.plus.tracker.tool.health),
- Camera PDF Scanner
(com.jiao.hdcam.docscanner).
Don haka ana ba mutane shawara da su kiyaye kansu, akwai wani Bature da yace idan kayi downloading app a Google play Store to ka tabbatar ka bincika information dinsa reviews da Kuma details na wanda ya kirkiri app don kaga shin Wanda ya dace ka dora a wayarka ne.
Don haka a daina granting permission ma app ko da kuwa ka yadda da source dinshi kawai notification ne ya dace Kai allow ga kowane app.
Comments
Post a Comment