Main menu

Pages

ILLAR RIKON FITSARI KASHI NA BIYU

 



MAFI YAWANCIN MUTANE BASU SAN RIKON FITSARI KE DA ILLA GA MUTUM BA (2)


Wasu kuma koda maza ne, idan girma ya fara kama su, gaɓɓansu musamman mafitsara kan fara ƙirƙirar halayyar saurin fitar da abinda ke cikin mara sakamakon ɓacin rai ko mummunar fusata. Abu mai muhimmanci gaske da ya kamata mutum ya sani shi ne, mutukar yana yawaita riƙe fitsari ba tare da zubar da shi ba akai-akai, to babu shakka yana cikin babban haɗarin kamuwa da cututtukan dake da alaƙa da mafitsara (UTI).



Wani abin lura kuma shi ne, ba rashin yin fitsari ne kawai ke iya haifar da matsalar mafitsarar ba; hatta rashin shan isasshen ruwa kan iya haddasa matsalar ta UTI, sakamakon babu isasshen fitsari a cikin marar da kwakwalwa zata karbi saƙon cewa lokacin fitsari yayi. A dalilin haka kuma sai a samu matsalar bayar da umarni da kuma sanin lokacin cewa fitsari yayi. Ga wasu alamomi da ya kamata a lura da su sosai, matukar ana fuskantarsu to wataƙila an yi arangama da matsalar ciwon mafitsara (UTI). Kuma lokaci yayi na zuwa ziyarci likita. Daga cikin alamomin akwai: Yawaitar jin fitsari Jin zafi yayin fitsari.



Canzawar kalar fitsari kamar kalar hadari Fitowar jini tare da fitsarin Jin raɗaɗi yayin fitsari Mafitsara na daya daga cikin sassan jikn dake taimakawa Mutum yin fitsari bayan koda ta tace ruwan da take bukata, a wasu lokutan, akan samu yanayin da fitsarin zai koma inda ya fito wato hanyar koda wanda kuma hakan babbar matsala ce.


maganar gaaskiya ita ce, maza garzaya kayi fitsari da zarar kaji bukatar hakan, kar kace har sai ya matseka balle ka rika matse shi har ya haifar maka da matsala. Amma idan babu makewayi kusa ko baka son fita daga inda kake, ga wasu yan dabaru da zaku amfani dasu da zasu ara muku lokaci kafin a samu zarafin yinsa.


daga cikin abubuwan dabaru da zaku iya yi wajen rike fitsari yayin da ya matseku akwai: Sauraren qur'ani musamman idan da bututun sautin kunne Cigaba da zama idan dama a zaune kake Karatun littafi Cigaba da duba sabbin labarai a shafukan sada zumunta Samun dimi ko kin zuwa waje mai sanyi zuwa ganin likita shi ne babbar dabara yayin da kake zargin kamuwa da cututtuka domin duba lafiyarka.

ABUBUWAN DA KE JAWOWA MATA JIN ZAFI YAYIN FITSARI

◆yawan rike fitsari amara

◆Yawan biyawa kanki bukata

◆Virus dayake kama mafitsara

◆Kamuwa da ciwon suga

◆Rashin kulada shan ruwa

★★★★★★★★★★★★★★★★★

HANYOYIN MAGANCE MATSALAR

◆kulada shan ruwa

◆Hada zuma da habbatussauda

◆Shan shayin hulba

◆Shayin BAQDUNAS.

Allah Ya sa a dace Ameen.


Comments