Main menu

Pages

KO KUNSAN ILLAR RIKON FITSARI KUWA (1)

 



MAFI YAWANCIN MUTANE BASU SAN RIKON FITSARI KE DA ILLA GA MUTUM BA


Mai dabi'ar matse fitsari yana cikin matsala - Matsalar ba ta tsaya kan yin fitsari a wando kawai ba, har ta kai ga lalata wasu sassan jiki - Amma masana sun bayar da shawarar yadda zabi don matse fitsarin na dan wani lokaci riƙon fitsari ba sabon abu ba ne ga mata ko maza, yara ko manya, hasali ma abu ne da ya zama ruwan dare. 



Shin ko kunsan cewa mafitsarar babban mutum na iya ajiyar fitsarin da yawansa bai wuce babban kofi biyu ne na ruwa ba kacal? Kuma da zarar ya haura hakan, zaka fara jin mutane na cewa fitsari ya matse ni.


Kunga kenan. zaku iya auna yawan adadin ruwa ko lemon da zaku sha idan zaku je wurin da babu makewayi. Ko kun taɓa tambayar kanku cewa ko riƙon fitsarin da kuke yi na da wata illa ga lafiyarku? A yau na kawo muku jerengiyar bayanai kan rike fitsarin da maza da mata kanyi a lokuta daban-daban bisa dalilai mabambamta. 



Duk da dai babu wata doka da ta nuna lallai-lallai ga lokutan da Mutum zai yi fitsari, amma yinsa da wuri ko akasin hakan ya ta'allaƙa ne ga yanayin halitta, kowa da kalar sa. Idan har Mutum na da sakakkiyar mara, da rike fitsari ke masa wahala to riƙon nasa bai wuce ace kamar ƙoƙarin horas da marar ne ba.



Amma a wasu lokutan riƙon fitsarin kan zama illa ga lafiya da kuma hadarin kamuwa da ciwon ƙoda, idan har kana da ɗaya daga cikin abubuwan da zamu lissafa a ƙasa: 

- Toshewa ko sirancewar bututun fitar fitsari 

-  Kakkatsewar fitowar fitsari 

- Matsalar koda 

- Raguwar fitsari a cikin mara 


Mata masu ciki na cikin babban haɗari mutuƙa, ga ciki ga kuma riƙon fitsari wanda na iya jawo ƙaruwar haɗarin kamuwa da wasu cututtukan.


To amma me yake faruwa da jikan Mutum idan ya riƙe fitsari? Bayanin dalilin da yasa Mutum yake jin fitsari ya wuce kawai don mara ta cika ne, abu ne mai wahalar ganewa, amma daga cikin abubuwan da suke faruwa ya haɗa da; wasu sassan jiki da gaɓoɓi tare da aiki da kwakwalwa sannan sai kaji cewa lokaci yayi na ayi fitsari.

Ga wasu matan yawaitar saurin yin fitsarinsu na ƙaruwa bayan sun fara haihuwa, wannan na faruwa ne sakamakon sauye-sauyen da halittun jikin nasu suka samu, ga kuma rauni da gaɓoɓin jikin suka yi.

Zamu cigaba a post na gaba.


Comments