Katafaren kamfanin harkokin fasaha na duniya Google, ya sanar da ƙara sabbin harsuna guda 24 a rumbunsa na fassara.
Matakin ya kawo jimillar harsunan da Google ke fassarawa zuwa 133.
Goma daga sabbin harsunan da Google din ya ƙara yaruka ne na al'ummar Afirka.
Yarukan Afirka da Google din ya kara sun hada da Lingala da Twi da kuma Tigrinya
Google ya ce ya dauki matakin ne domin taimaka wa wadanda yarukansu ba sa kan yawancin shafukan fasaha.
Sauran yarukan da ya kara sun fito ne daga al'ummar Bhojpuri wanda mutum miliyan 50 a arewacin India ke amfani da shi, da Nepal da kuma Fiji wadanda su ma akwai masu amfani da su da dama.
A shekarar 2020 ne Google ya ƙara yaruka biyar.
Don haka sai ayi ta shiga Google don yin searching fassaran Wani yare da kakeson sanin ma'anarsa.
Comments
Post a Comment