A ranar biyar ga watan Mayun 2022 ne tsohon shugaban Najeriya Marigayi Umaru Musa Ƴar'Adua ya cika shekara 12 da rasuwa.
Shugaban ya rasu ne a ranar biyar ga watan Mayun 2010 bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.
Kafin rasuwarsa, ya sha kai da komowa zuwa kasar Saudi Arabia domin neman lafiya wanda har a wannan lokacin hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya.
Bayan rasuwarsa, mataimakinsa Goodluck Ebele Jonathan ne ya gaji marigayi Umaru inda ya shafe shekara shida kan karagar mulki
Dangane da cikar marigayi Umaru Musa Yar'Adua shekara 12 da rasuwa, jama'a da dama a shafukan sada zumunta na tunawa da shi da kuma ci gaba da gudanar da ta'aziyya ga Najeriya da kuma iyalansa bisa rashin da aka yi.
Rasuwar Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua
Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar'Adua ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayun 2010 bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.
A lokacin da ya rasu, tashar talabijin ta tarayya da ke kasar ce ta bayyana rasuwar shugaban a daren Talata 5 ga watan Mayu.
Bayanin rasuwar shugaban na Najeriya Umaru Musa Yar'Adua ya jefa kasar cikin wani hali na tunani game da salo da batun mulki da kuma harkokin siyasar kasar za su dauka.
A ranar 6 ga watan Mayun 2010 ne aka yi jana'izar tsohon shugaban a mahaifarsa da ke Jihar Katsina inda jana'izar ta samu halartar manyan mutane daga sassa daban-daban na Najeriya.
Marigayin ya rasu ya bar mace Ɗaya Hajiya Turai Yar'Adua da ya'ya tara, biyar mata huɗu maza.
Yaransa uku mata sun auri tsoffin gwamnonin Bauchi da Kebbi da Katsina.
Marigayi Umaru Yar'Adua shi ne shugaba na biyu da ya karbi ragamar mulkin kasar bayan komawarta ga turbar Demokradiyya a shekarar 1999.
Kuma ya karbi ragamar mulki ne daga hannun Shugaba Olusegun Obasanjo bayan wani zabe mai cike da taƙaddama a shekara ta dubu biyu da bakwai.
Mulkin Shugaban
Bayan hawan shi kan karagar mulki, shugaban ya fito da sabon salon mulki inda ya fito da manufofi bakwai da yake gani zai yi amfani da su domin tsallakar da kasar zuwa ga tudun mun tsira.
Waɗannan manufofi da aka yi wa lakabi da ''7 point agenda'' a turance sun hada da :
1- Habaka wutar lantarki
2- Wadatar da kasa da abinci
3- Habaka arzikin kasa
4- Ingantan harkokin sufuri
5- Garanbawul kan yadda ake mallakar filaye
6- Samar da tsaro
7- Inganta Ilimi
Waɗannan su ne abubuwan da shugaban ya sa a gaba a wancan lokaci, sai dai yana cikin gudanar da waɗannan ayyuka rashin lafiya ta kama shi.
Duk wadannan abubuwan da yayi da Wannan qaunar da aje masa da taba masa bisa namijin kokarin aikin da ya faro duk fa yayi sune a cikin shekaru biyu kacal da hawanshi, yin ayyukan ma bai Kai Shekara biyun ba saboda doguwar jinyar da yayi kenan aikin yayi shine cikin Shekara daya da 'yan wasu watanni.
Yau gashi shekaransa 12 da rasuwa Amma 'yan Nigeria sun kasa manta tarin ayyukan da yayi na Shekara daya kacal. Subhanallah tsarki ya tabbata a gareKa Ya Allah.
Yaa Allah Ka jikan Umar Musa 'Yar adua Yasa Aljannah Firdausi ce makonar shi. Allah Kayi mana zabin shugaba nagari adali irin Umar Musa 'Yar adua ko ma wanda yafi shi. Allah Kayi mana tsari da azzaluman shugabanni Ya Hayyu Ya Qayyum Ameen.
Comments
Post a Comment