Yadda Ake Gyaran Jiki Da Gwaiba:
Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na kwalliya tare da fatan ana cikin koshin lafiya?
Sau da yawa za a ga ba a cika damuwa
da wannan nau’in ’ya’yan itacen ba. Ba don wani abu ba ne illa don yawan kananan kwallon da ke cikinsa.
Shin ko kun san cewa gwaiba tana da matukar inganci a wajen gyaran jiki da gashi?
To in ba a sani ba sai a dage a karanci abin da na rubutu muku a yau.
Gwaiba na mayar da fatar tsohuwa yarinya; ’ya’yan itacen nan na dauke ne da sinadaran bitamin A da B da C.
Wadannan sinadaran na taimaka wa fata zama sabuwa a kodayaushe.
Kullum suna cikin mayar da ita mai sulbi da kuma laushi kamar ta ’yan mata.
Tana dada hasken fata; sakamakon sinadaren da ke dauke a cikin gwaiba,
tana dada hasken fata kuma tana taimakawa wajen hadar da fata.
Za a iya daka ganyen gwaiba sai ana wanke fuska da ita domin magance kurarrajin fuska da kuma dada hasken fata.
Yawan cin gwaiba na dada tsawon gashi;
A sami gwaiba nunanna akalla kamar sau uku a rana. Yawan cinta na taimaka wa tsirar gashin kai. Kuma gashi na daya daga cikin ababen da ke kara wa mace kyau.
Gwaiba na dauke da sinadarin folic acid wanda ke taimaka wa mata masu juna biyu.
Yawan cin gwaiba na taimakawa wajen girma ga dan da ke cikin mahaifiyarsa kamin haihuwa.
Comments
Post a Comment